Idin Babbar Sallah: Masu raguna sun koka da rashin kasuwa

Idin Babbar Sallah: Masu raguna sun koka da rashin kasuwa

– Yayin da ake shirin Bikin babbar Sallah, masu raguna na ta kara kokawa game da rashin kasuwa

– Legit.ng sun ziyarci Kasuwannin Legas kamar kasuwar kara (ta dabbobi) da ke Adekunle da ta Mile domin ganin yadda irin wainar da ake soyawa

– ‘Yan kasuwa suna kukan rashin ciniki, kowa dai na kukan babu kudi a Kasar

Idin Babbar Sallah: Masu raguna sun koka da rashin kasuwa

 

 

 

Ga shi Sallah ta karaso, sai dai masu raguna fa na ta kukar rashin ciniki! Legit.ng sun tabbatar da hakan bayan sun zagaye wasu kasuwanni domin jin ta bakin su. Musulmai na dai yanka dabbobi da sallah a mastayin ibada ko ina a duniya, don haka muka zagaya kasuwannin kara da ke Kasar. Sai dai rashin kudi da ake fama da shi a Kasar ya tusa kowa gaba.

Matsalar rashin kudi ya hana mutane da dama sayen raguna wannan karo, duk da cewa dai ragunan hawa-hawa ne watau iya kudin ka, iya shagalin ka! Akwai na daidai kudin mutum, mai araha. A kasuwar dabbobi ta Adekunle sun tabbatar da lallai cewa an samu ‘canji a Najeriya’. Wani daga cikin masu harkar saida raguna yake cewa ya kai kusan shekara 30 yana wannna aiki, bai taba ganin abubuwa sun sauya ba, sai wannan karo, ko in aka taba, babu kudi! Ana ta hakuri ne kawai.

KU KARANTA: Matsalar rashin Kudi; Bukola Saraki yace ayi ta addua

Ana saida ragunan ne a kan kudi N35,000,N40,000 ko kusa da haka. Banbancin da na bara bai wuce N5, 000 zuwa N10, 000 ba. Saboda abubuwa sun tashi yamzu. Sun bayyana cewa ciyar da raguna ma bayan an saye su kawai wani aiki ne, saboda halin da ake ciki a Kasar. Kudin kawo raguna ya tashi ne, a cewar ‘yan kasuwan. Yanzu sai kuma a dauki mako guda rago na hanya, ba kamar yadda aka saba ba (cikin kwana 2-3), yanzu fa babu kudi ko ina...Inji su.

Amma dai masu kasuwanni suna kuka kwarai da gaske, saboda rashin ciniki. Watakila kuma a yau abubuwan su canza, don wasu sun fi son sayen raguna ana daf da Sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel