Ba dole a Layya -Malamin Musulunci

Ba dole a Layya -Malamin Musulunci

Yayin da Sallah ta matso, hankalin magidanta ya koma ga yadda za su samu su yi Layya, Sai dai wani Shehin Malami a Kano ya ce Layya ba wajibi ba ne

Ba dole a Layya -Malamin Musulunci

Wani Shehin malami mai wa’azin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa ya ce, yin Layya ba wajibi ba ne, don haka ba sai mutane sun kallafawa kansu na sai sun yi a cikin halin matsi ba.

Shehun Malamin ya bayyana haka ne a wani shirin Rediyo, a inda ya ke amsa tambayoyin masu sauraro, wanda kuma ake yadawa a gidajen Rediyon jihar, a ranar Lahadi 9 ga watan Satumba, ya kuma ce, ibadar layya sunna ce mai karfi amma ga wanda ya samu iko.

Malamin wanda ya janyo hadisai don kafa hujja da fatawar ta sa, ya kuma ce, akwai wasu manyan Sahaban Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da suka ki yin Layya a wasu lokuta, duk da cewa suna da iko, a zamaninsu, kawai don su nunawa jama’a rashin wajibcinsa.

Shehin malamin wanda kuma shi ne babban kwamandan Hisbah a jihar Kano, ya yi magana kan rashin dacewar mutum ya ci bashi don ya yi Layya, da yin Layya don kar yara su shiga wani hali, da sauran wasu furucin da jama’a ke yi wadanda aka iya sa su rasa ladan ibadar yankansu.

A Najeriya ana fama da matsin tattalin arzkin da ta kai abincin da za a ci sau uku a rana na gagarar mutane da yawa a kasar, sannan ga kuma bukatar yin Layya a yayin bikin Sallar Idi da za a gudanar a ranar Litinin 12 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel