Idan ba tsoro ba, ka tafi Amurka mana-NYM tace da Kashamu

Idan ba tsoro ba, ka tafi Amurka mana-NYM tace da Kashamu

Idan ba tsoro ba, ka tafi Amurka…-Kungiyar Arewa tace da Kashamu

Idan ba tsoro ba, ka tafi Amurka mana-NYM tace da Kashamu

 

 

 

Wata Kungiya ta matasan Arewa na son ganin an yankewa Sanata Buruji Kashamu hukunci

Wata Kungiya ta matasan Arewacin Najeriya ta dauki nauyin kudin jirgin Sanata Buruji Kashamu zuwa Kasar Amurka, inda ake zargin Sanatan da safarar kwayoyi. Kungiyar tana so Buruji Kashamu ya je Kasar ya wanke kan sa. Kungiyar mai suna ‘Northern Youths Movement’ (NYM) tace abin da ya fi dacewa da Kashamu, ya je Kasar Amurka ya wanke kan sa daga zargin da ake yi masa, ba ya tsaya a Najeriya, yana amfani da Kotu domin a hana kama sa ba.

Kungiyar matasan tayi alkawarin saya wa Kashamu tikitin jirgi zuwa Kasar Amurkar inda ake zargin sa da laifin harkar kwayoyi. Shugaban Kungiyar ta NYM, Mallam Ishaya Jato, ya bada wannan jawabi. Mallam Jato ya kara da cewa Kungiyar matasan za ta dauko nauyin wurin kwanan Sanatan da kuma ci da shan sa a Kasar har ya dawo gida. Wannnan Kungiya ta kuma gargadi Alkalan Kasar nan wajen zartar da sharia’ar su, Kungiyar ta ja kunnen musamman Alkali Okon Abang da wasu, inda ta zarge su ma da karbar cin hanci daga hannun Sanata Kashamu. Kungiyar tace Alkalan Kotun su daina bada hukuncin da za su hana a tafi da shi (Kashamu) Amurka inda ake tuhumar sa.

A cewar Kungiyar idan har Kashamu yana da gaskiya, ba zai tsaya bin Kotunan Kasar nan ba domin su sa a hana kowa ya taba sa. Sanata Buruji Kashamu dai ya sha nanatawa cewa ba shi da laifi a zargin da ake yi masa, sai dai matasan sun ce idan gaskiya ce, ya je ya fadawa Amurka hakan. Kashamu dai yayi da’awar cewa dan uwan sa (wanda suke matukar kama) ya aikata wannan laifi ba kuwa shi ba, sai dai Kungiyar NYM tace Kashamu yaje Amurka ko da na kwanaki uku ne, sai a gane cewa ko har abin da yake fada gaskiya ne.

KU KARANTA: Kasar Amurka tayi kira ga Shugaba Buhari

Shekarar bara dai Kungiyar yaki da kwayoyi na Kasa watau NDLEA tayi yunkurin kame Sanata Kashamu, sai dai hakan bai yiwu ba.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel