Onuesoke ya caccaki Gwamna Masari

Onuesoke ya caccaki Gwamna Masari

-Wani jigon PDP Onuesoke yayi kaca kaca da gwamna Masari domin sukar tsohon shugaba Goodluck Jonathan kan rikicin Neja Delta

-Masari yace Jonathan yayi shekaru shidda yana mulki ba tare da ya raya yankin Neja Delta ba duk da kudaden mai masu yawa da aka samu

-Amma a cewar Onuesoke, Jonathan shugaba ne na kasar baki daya, saboda haka bai bada fifiko ga wani yanki ba fiye da wani

Onuesoke ya caccaki Gwamna Masari

Chief Sunny Onuesoke, wani tsohon dan takarar gwamna a jihar Delta, yayi kaca kaca da gwamnan jihar Katsina Aminu Masari dalilin sukar tsohon shugaba Goodluck Jonathan

Ranar Talata 29 ga Agusta, Masari yace tsawon shekaru shidda dan Neja Delta yana shugaba amma ya kasa kawo cigaba a yankin duk da makudan kudade da aka samu daga mai. Duk da Masari bai ambaci sunan wani ba, amma daya ce shugaba dan Neja Delta an san da Goodluck Jonathan yake

A wani jawabi da yayi a Warri, Onuesoke ya maida ma Masari martani inda yake cewa kamata yayi Masari yayi wannan zargin ga dattawan arewa wadanda suka mulki kasar kusan shekaru 56 na rayuwar kasar amma ba wani abin azo a gani a kasar. ya cigaba da cewa ba wani abu face rashin cingaba, talauci da jahilce a arewacin kasar a cikin shekaru 56. Onuesoke ya lissafta abubuwan cigaba da aka samu cikin shekaru shidda da Jonathan yayi yana mulki. Yace yaci nasara wajen canza fuskar kasar a bangarori irin su wutar lantarki, gyaran da kuma fadada ayyukan raya kasa, aikin noma, ilmi da kirkiro ayyuka a cikin abubuwa da dama.

KU KARANTA : Yan siyasa ke daukan nauyin makiyaya dake kai hare hare – Jigon APC

Yace, yayin da shi Jonathan dan Neja Delta ne, ya maida hankali wajen raya arewacin kasar da sauran bangarori domin ya dauki kasar duka tamkar kasarsa. Ya Kara da cewa:

"An Sami gagarumin cigaba wajen ilmi inda aka kafa jamio'in tarayya 12, inda hudu daga cikinsu suna garuruwan Dutsinma a Katsina, Dutse a Jigawa, Gusau a Zamfara da Birnin Kebbi a Kebbi, wadanda ke bangaren arewa maso yamma, yayin da aka Gina makarantu 125 na almajirai domin bada ilmi ga marasa galihu."

Masari dai ya kalubalanci tsohon shugaba Jonathan da sauran shuwagabannin Neja Delta da su fito suyi bayanin yadda suka sarrafa dukiyar kasar. Ya cigaba da cewa dalilin facakar da gwamnatin PDP tayi ya jaza wasu jihohi basa iya biyan albashin ma'aikatansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel