Najeriya ka iya kamuwa da cutar Zika- bincike

Najeriya ka iya kamuwa da cutar Zika- bincike

- Zika wata cuta ce da cizon sauro ke haddasawa mussaman ga jarirai

- Yan Najeriya ka iya kamuwa da cutar Zika

- Cutar na haifar da zazzabi mai zafi, ciwon kai da kuma ciwon gabobbi (jiki)

- Wasu kasashe sun shawarci mata da kada su dauki ciki

Najeriya ka iya kamuwa da cutar Zika- bincike
cizon sauro ke haddasa cutar Zika

Cutar Zika, wata cutar cizon sauro ce da ta yadu da sauri cikin kasashe da dama, kuma tana iya yaduwa a fadin kasar Amurka, Landan harma da kasar Najeriya, kungiyar lafiya ta duniya (WHO) tayi gargadi.

A cewar kungiyar lafiya ta duniya (WHO), cutar Zika, wacce ke afkuwa sakamakon cizon sauro, yawanci yana haddasa zazzabi mai zafi, kuraje, ciwon jiki da kuma ciwon kai, an riga an gano cutar a kasashen Asiya, Arewacin Amurka da Kudanci ta.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta mutu a jihar Edo

An gano cewa an haifi dubunnan jarirai wanda kwakalwarsu bai cika ba, wanda hakan ne yasa wasu kasashe suka shawarci mata da kada su dauki ciki.

Jaridar Guardian ta bayyana cewa kasar Najeriya, wacce tana daya daga cikin kasashen dake fama da cutar cizon sauro, tana iya kamuwa da cutar Zika.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel