Matasan Enugu sunki amincewa da kai hari ga makiyaya

Matasan Enugu sunki amincewa da kai hari ga makiyaya

-Matasan jihar Enugu sun ki amincewa da kiran da wasu mutane keyi na cewa su gudanar da harin daukar fansa a kan Fulani makiyaya

-An zargi makiyayan da kai hari a wasu kauyuka a jihar

-Matasan sunce duk wani matakin gaggawa zai shafi rayuwar Inyamurai dake arewa

Bayan kisan mutanen jihar Enugu da wanda ake zargin Fulani Makiyayane suka aikata kisan, matasan jihar Enugu sun kin amincewa da wadanda suka yi kira kan cewa a kai masu harin ramuwar gayya.

Fulani Makiyaya sunyi ta’addanci a wasu kauyukan jihar Enugu kuma wannan ne yayi sanadiyar da wasu dalibai da matasa sukayi kira kan a dauki mataki mai tsanani a kan makiyayan.

Sabon harin da suka kai yayi sanadiyar mutuwan mutane biyu, yayinda mutane uku suka ji raunuka, kuma wasu da dama dun bukaci matasa da su dauki makamai a kan makiyayan.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC na jihar Ondo

Jaridar Vanguard ta kuma ruwaito cewa kungiyar daliban Najriya, wato National Association of Nigerian Students (NANS) babin jihar Enugu sunce ba daidai bane daukar mumunan mataki.

Sun bayyana cewa hakan na iya haifar da da mara ido kuma zai iya sanadiyar saka rayukan matasa da yan makaranta cikin hatsari a jihar.

Sunce ba kamar jihar Ekiti ba, yawan inyamurai dake zaune a arewa yana da yawa kuma bazasuyi abunda zai sa rayuwansu da dukiyoyinsu a cikin  hatsari ba.

Sun shawarci gwamnatin jihar da yayi kira ga taron gaggawa domin a wayar da kan mutane kan yadda zasu kare rayukansu da dukiyoyinsu.

KU KARANTA KUMA: Malami ya ba dalibinsa kyauta

Sun kuma nuna yardarsu a kokarin gwamnatin jihar kan tabbatar da cewa anyi adalci a kan al’amarin makiyaya.

Sunyi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro da su dauki mataki domin kawo karshen ayyukan makiyaya a kasar baki daya.

A kwanaki biyu da suka wuce, munji cewa Mambobin Kungiyar Civil Liberties Organisation (CLO) sun zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanya hannu a cikin hare-haren da Fulani makiyaya suka kai jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel