Kotu ta dakatar da gasar NPFL

Kotu ta dakatar da gasar NPFL

– Wani Babban Kotu a garin Jos ya dakatar da NPFL saboda ta ki dawo da kungiyar Giwa FC

– An dakatar da Kungiyar Giwa FC ne bayan ta ki buga wasanni har uku a jere

– Kotun ta bada umarnin a dawo da Kungiyar cikin Gasar a baya

– Sai dai Hukumar da ke kula da Gasar tayi watsi da umarnin kotun

Kotu ta dakatar da gasar NPFL

Wata Babbar Kotu da ke Bukuru, a Garin Jos ta da dakatar da Wasannin Najeriya (NPFL) bayan Kwamitin da ke kula da wasannin sun yi watsi da umarnin da ta bada a baya.

KU KARANTA: Aubameyang na son zuwa Real Madrid

Wata Kotu a Garin Jos na Najeriya ta dakatar da Gasar wasannin gida (NPFL) har sai Inna-ta-gani, wannan dakatarwar ta zo ne bayan Kungiyar LMC da ke kula da Gasar tayi watsi da umarnin kotu. A baya dai Kotun ta bada umarnin cewa a dawo da Kungiyar Giwa FC cikin Gasar ta NPFL. A jiya ne dai wannan Kotu ta yanke hukuncin, haka kuma na nufin cewa za a tsaida wasannin a mako na 32.

Kotun dai ta bada umarnin dawo da Kungiyar Giwa FC cikin Gasar NPFL ta Kasa can baya, sai dai kuma har yanzu ba ayi hakan ba. Hakan ta sa Kungiyar ta kara garzayawa Kotu domin sanar da ita abin da ke faruwa. LMC mai kula da wasannin dai tace za a cigaba da gudanar da wasanni kamar yadda aka dais aba, don kuwa babu wata takarda daga kotu da tace a tsaida wasannin.

Alkali Kunda wanda ya zartar da wannan hukunci y ace Hukumar LMC tana kokarin jan lokaci ne kurum, saboda ayi maza a kammala Gasar kafin a gama shari’ar. Alkalin y ace Hukumar na iya daukaka kara idan tana bukata. Sai dai Hukumar tace ita fa babu wanda yace ta dakatar da wasannin ta a duniya.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel