Jami'an tsaro sun kashe wasu 'yan adawa' biyu

Jami'an tsaro sun kashe wasu 'yan adawa' biyu

- Mutumin da shugaban Gabon Ali Bongo ya kayar a zaben ranar Asabar

- Jean Ping, ya ce jami'an tsaro sun shiga hedikwatar jam'iyyarsu, a inda suka kashe mutum biyu sakamakon bude wuta.

Jami'an tsaro na kasar dai sun kai wani samame hedikwatar jam'iyyar, bayan zargin wasu bata-gari da cinna wa majalisar dokokin kasar wuta.

Dan takarar jam'iyyar adawa da aka kayar, Jean Ping ya ce an kashe mutane biyu sakamakon harbi da jami'an suka yi.

Magoya bayan Ping dai suna ta faman zanga-zanga tun bayan fitar da sakamakon zaben da aka yi wanda ya nuna shugaba Ali Bongo ne ya lashe zaben.

Masu zanga-zangar dai suna zargin gwamnati ne da yin magudi.

Sakamakon zaben dai wanda aka sanar ranar Laraba, ya bayyana shugaba Bongo da wanda ya yi nasarar lashe zaben da kaso 49.8, a inda shi kuma Jean Ping ya samu kaso 48.2.

Asali: Legit.ng

Online view pixel