An tsige shugabar kasar Brazil Dilam Rouseff

An tsige shugabar kasar Brazil Dilam Rouseff

Karshen tika tika tiki, a jiya ne majalisar dattijai ta kasar Brazil ta kammala tsige shugabar kasar Dilam Rouseff daga karagar mulki biyo bayan dakatarwar data mata.

An tsige shugabar kasar Brazil Dilam Rouseff

Sai dai uwargida Dilma tace tsigetan da aka yi tamkar juyin mulki ne.

Sanatoci 61 ne suka goyi bayan a tsige uwargida Dilma, inda aka samu sauran sanatoci 20 dake nuna rashin amincewarsu da tsige Dilma, wanda hakan ya baiwa yan adawa rinjaye da na kaso 2 bisa ukun da ake nema wajen tsige shugabar kasar.

BBC ta ruwaito cewa a yanzu dai Michael Termer ne zai rike shugabancin kasar Brazil a matsayin rikon kwarya inda zai kareshe sauran wa’adin mulkin Dilma Rouseff da zai zo karshe a ranar 1 ga watan janairu na 2019.

Majalisar dattijon kasar Brazil ta tsige Dilma Rouseff ne kan kamata da laifin yin aringizon kasafin kudi da ta yi. Hakan ya sanya majalisar dakatar da shugaba Dilma a watan mayu daga gudanar da al’amuran mulki har sai sun kammala bincike akan ta. Sai a jiya 31 ga watan agusat ne majalisar ta yanke shawarar tsige ta daga kan mulki.

Kamar yadda rahoton BBC ya nuna, yan adawar Dilma sun ce tayi kokarin cike gibin kurakuran da aka samu ne wajen gudanar da tsare tsaren dadada ma yan kasa ne saboda a sake zaben ta a karo na biyu.

Sai dai uwargida Dilma Rouseff ta musanta zargin da ake mata, inda ta kwatanta tsigewar da juyin mulki, tsige ta da aka yi ya kawo karshen mulkin jam’iyyar ma’aikata da ta kwashe shekaru 13 kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel