An zargi Buhari da daukar nauyin harin makiyaya

An zargi Buhari da daukar nauyin harin makiyaya

-Mambobin Kungiyar Civil Liberties Organisation (CLO) sun zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanya hannu a cikin hare-haren da Fulani makiyaya suka kai jihar Ekiti

-Kungiyar sun bayyana bacin ransu kan rashin kama su bayan kisan kiyashin da makiyaya sukayi ga yan unguwa 13 a Nimbo a ranar 25 ga watan Afrilu

An zargi Buhari da daukar nauyin harin makiyaya
Fulani makiyayi dauke da bindiga

Haushin cewa gwamnati bata sanya baki gurin maganin rikicin Fulani makiyaya a jihar Ekiti ba, yasa kungiyar Civil Liberties Organization (CLO) sun yanke shawarar cewa sakachin da  shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi yana iya yiwuwa yana da hannu a cikin hare-haren koma killa shi ke daukar nauyin su.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta kara kudin shigar motoci filin jiragen sama(Hoto)

Kungiyar ta jadadda cewa abu irin wannan yana faruwa a wata kasa a nahiyar Afrika, Turai ko wani bangare a duniya, da Buhari ya kasanace cikin mutane na farko da zasu fara sukar kashe- kashen amma yana yi kamar babu abunda ke faruwa a kasar sa.

har ila yau, kungiyar CLO sun nace a kan lura da kamu da kuma hukunta Ibrahim Adamumale, 20, wani Fulani makiyayi da ake zargi, an kama a Affa, karamar hukumar Udi dake jihar Enugu, da laifin samunsa da bindigar AK-47 tare da alburusai 24.

KU KARANTA KUMA: Wani matashi ya tashi bayan likitoci sun tabbatar da mutuwarsa (Hotuna)

Bayan haka, kungiyar sunyi Allah wadai da tserewar wasu yan kungiyar da aka kama kan zargin kisan kiyashi a Nimbo a ranar 25 ga watan Afrilu, inda aka kashe yan garin guda 13 duk da sahihanci a idanun fasaha.

Wandanda aka kama kan zargin harin Nimbo sune: Mohammed Zurai, Ciroma Musa, Sale Adamu, Suleiman Laute da kuma Haruna Laute.

Asali: Legit.ng

Online view pixel