Labari da dumi-dumi: rikici ya kaure a gidan yarin Kuje, ana barin wuta

Labari da dumi-dumi: rikici ya kaure a gidan yarin Kuje, ana barin wuta

-An rubuto wasu hargitsi a gidan yarin Kuje a farkon ranar Litinin, 29 ga watan Augusta

-An rahoto cewa ana ta musayyar wuta a lokacin da abun ke faruwa

-Jami’an tsaro na kokarin ganin sun dawo da zaman lafiya a gurin

Labari da dumi-dumi: rikici ya kaure a gidan yarin Kuje, ana barin wuta
Gidan yarin Kuje

Hujjoji sun bayyana cewa rikici ya kaure a gidan yarin kuje a safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Augusta, a lokacin da jami’an gurin suka isa gurin domin tafiya da al’amuransu nay au da kullun.

Wani babban jami’I, wadda baza’a iya ambatan sunan sa ba saboda ba’a bada umarnin yin hakan Magana kan al’amarin ba, ya fada wa manema labarai cewa rikicin ya fara ne da misalign karfe 10.30 na safe daga bangare daya har ya yadu zuwa sauran bangarorin.

Yace an kawo tawagar jami’an tsaro ginin dake dauke da yan tawayen amma ba ba’a sani ko wasu sun tsere ba.

Wani majiya ya bayyana cewa an rufe yan fursuna yayinda jami’an tsaro suka harba barkonon tsohuwa a kusa da inda aka rufe fursuna din.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin kurkukun Najeriya, Francis Enobore, ya tabbatar da faruwa lamarin a lokacin da aka kira shi.

KU KARANTA KUMA: Ngige ya bukaci matasa da su shiga shirin da gwamnati ta tsara

An samu yawan fashe-fashen gidan yari a cikin yan lokutana nan.

A ranar 30 ga watan Yuli, yan tawaye 13 ne suka tsere daga kukrkukun Koton Karfe a jihar Kogi.

Bayan kwanaki 10, wasu yan tawaye 15 sun kuma tserewa a gidan yarin tarayya dake NSUKKA, jihar Enugu, a wani fasa gidan yari da aka rahoto ya faru da yamma.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel