Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar Kusugu Da Labarin Bayajidda

Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar Kusugu Da Labarin Bayajidda

Tarihin Hausa ya nuna cewa sama da shekaru 2000 da suka wuce, al'ummar Hausawa na zanne a tsakiyar kasashen bakaken fata wanda ya kasance a Arewacin Najeriya da wani sashen Nijar a yanzu.

[article_adwert]

Daura na daya daga cikin manya manyan kasashen Hausa a lokacin. Tana da mata a matsayin Sarauniya, Wadanda suke mulki a wancan lokaci.

A lokacin Sarauniya Daurama, akwai wata rijiya mai suna Kusugu, wadda itace babbar rijiya dake ba garin Daura ruwa a wancan lokacin. Amma mutane basu samun bar ruwan saboda akwai wata Macijiya a cikin rijiyar.

Haka mutanen garin suka cigaba da zama har shaida wata rana wani mutum wanda ake tsammanin Dan Sarkin Bagadaza, Abu Yazid ya zo Daura bayan da ya kasa samun Sarki bayan mutuwar baban shi.

Jarumin Dan Sarkin bayan daya sauka gidan wata tsohuwa mai suna Ayyana, sai ya bukaci a bashi ruwa ya sha. Ruwan da aka bashi bai ishe shi ba, shi da mutanen shi. Sai ya roki tsohuwar data nuna mashi inda rijiyar garin take domin ya ibo ruwan. Tsohuwar sai ta gargade shi akan Macijiyar amma bai ji ba. Bayan da yaje ibo ruwan sai sukayi artabu da Macijiyar inda ya kashe ta.

Ganin haka ya sanya Sarauniyar ta aure shi inda ya zama Sarki. Saboda baya jin Hausa ada ne ya sanya mutane ke ce mashi Bayajidda. Watau, Bayajjida.

Ya haifi yara bakwai wadanda sune sukayi mulkin kasashen Hausa guda bakwai.

Shugaban kasar Najeriya mai ci, Muhammadu Buhari dan asalin Daura ne, kuma yana da gida a can. Kuma yana da sarautar Bayajidda Na Biyu a masarutar Daura.

Zuwan wakilin Legit.ng Daura ya samu dauko wasu hotuna na musammman na Rijiyar Kusugu da Fadar Sarkin Daura:

Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar Kusugu Da Labarin Bayajidda
Hoto tsohon fadar Daura
Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar Kusugu Da Labarin Bayajidda
Tsohon Sarkin Daura
Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar Kusugu Da Labarin Bayajidda
Gidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Daura a jihar Katsina
Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar Kusugu Da Labarin Bayajidda
Fadar Sarkin Daura a jihar Katsina

Source: Legit.ng

Online view pixel