Manya Manyan Labarai Guda 9 Da Suka Faru A Ranar Litinin 27

Manya Manyan Labarai Guda 9 Da Suka Faru A Ranar Litinin 27

Legit.ng ta tattara maku labarai masu amfani, kayatarwa wadanda suka faru a ranar 27 ga watan Yuli. ku duba domin ku samu duk abunda kuke so ku sani.

1. "Eh, ina so in balla NNPC" - Buhari

Shugaba Buhari ya tabbatar da rahotanni cewa, yana niyyar ya balla Kamfanin Mai na kasa. Dan siyasar yace, karancin mai yana daga cikin abubuwanda da gwamnatin shi keso ta magance a inda yayi magana a wani shirin da akayi dashi a ranar litinin a talabijin

2.Karshen Boko Haram yazo - Manjo Janar

Manjo Janar Nasiru Mu'azu bayana cewa yanzu yan Boko Haram basu iya fito na fito da sojojin Najeriya a wajen gumurzun da akeyi a Arewa masu Gabas. Yace: "Ina iya cewa babu tababa yan Boko Haram basu iya fuskantar sojojin Najeriya, na kuma maimaita, basu iyawa tabbas".

3. Yadda shugaban kasa ke shirin yin sulhu da yan Boko Haram.

Bayan an fara tattaunawa tsakanin shugaba Buhari da wasu shugabanni Boko Haram, fatan kubutar sama da yan matan Chibok 200 nata karuwa. Wata babbar majiya ce daga fadar shugaban kasa ta bayyan hakan.

4. Zuwan Amurka: PDP ta zargi Buhari da zubadda mutuncin Najeriya.

"Yanzu tafiyar tazo kuma ta wuce, amma abunda muke ji ma tsoro shine, babu wani abu da suka koya ko kuma aka amfana dashi. Abunda kawai muke samu a matsayin mu na Kasa shine, kunyatarwa, zargi, maida zargi,  da kuma gardamawa akan abubuwa masu amfani saboda rashin iya tafiyar da mulki da gwamnatin APC mai ci keyi."

5. Abunda yasa Yusuf Buhari ba zaya zama Janar na Soja ba -  Cewar Buhari.

Mai taimakama shugaban kasan akan harkokin hudda da jama'a Garba Shehu ya rubuta wani labari a inda yake bayyana cewa, lokacin da Shugaba Buhari ya hadu da abokan makarantarsu na Amurka, wasu dada ciki sun tambaye shi ko zaya bar dandanshi Yusuf ya Shiga Soja. "Ni na hana shi" inji Cewar Buhari.

6.  Abun takaici: wani Kwamishinan INEC mai shekaru 67 ya yasu.

Farfesa Mutala Salau ya rasu bayan yayi fama da rashin lafiya. Ya rasu ne a asibitin Turkish dake a Abuja. Lai Olurobode wani Kwamishinan na INEC yace, Salau wani mutum me abun kwaykwayo Wanda yake sanya ma mutane azama da murmushi a fuskokins Idan yana hudda dasu.

7. Wani Jariri dan watanni 18 ya bacce a lokacin da ake rada mashi suna.

Mutanen Inuosegba dake Abeokuta sun Shiga rudani bayan da aka gane Jaririn da ake rada ma suna ya bacce.

8. Alison Maduekwe na fama da wani matsanancin ciwo, dangin ta sun roki yan Najeria.

Tsohuwar Minista na fama da wani ciwo wanda ba'a san ko minene ba, a Inda aka kwantar da ita a wani asibiti a Landan. Dangin ta suka ce: "Yanzu diyarmu an kwantar da ita a asibiti ana duba ta tun satuttukan da suka wuce. Mun samu labarin cewa ana bi kwab wajen nasarin lafiyarta. Banda iyalinta na kusa, duk satututukan nan bata samu ganin kowa ba."

9. Rikicin majalisa. Taron da aka gudanar tsakanin Buhari da wasu yan Jam'iyyar APC bai samu cimma nasara ba.

A jiya ne 27 ga watan Yuli, Shugaba Buhari da Dogara sukayi wani zama a fadar shugaban kasa. Taron dai bai haifar da wani Da' mai ido ba Inda kowa ya toge a matsayar shi.

10. An gano shuwagannin kasan guda 10 na Afirika wadanda aka fi biya kudin Albashi.

Afirika Nahiyace dake da albarkatun kasa. Shin kun San tsananin arzikin wasu shuwagabannin kasashen? Ku duba domin ku sani.

11. Ka duba abinda Dan' Tiwa Savage ya samu.

Mai hada Kayan alatu Michael Awujola tabi sahun yan Najeriya wajen taya Tiwa Savage murnar haihuwar danta na fari jiya.

Source: Legit.ng

Online view pixel