Iya ma Najeriya sai Allah inji shugaba Buhari

Iya ma Najeriya sai Allah inji shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Allah ne kadai zai hade kan Najeriya

- Kamar yadda shugaban ya ce, ba abu ne mai sauki ba mutane su hade kansu a kasa wadda take da yaruka sama da 450

- Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Talata a yayin da yake kaddamar da Jami'r Edo dake Iyambo a karamar hukumar Etsako a jihar Edo

Iya ma Najeriya sai Allah inji shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A wani labarin kuma, gwamnatin Najeriya na samarwa da rundunar sojojin ruwan kasar manyan jiragen yaki na zamani.

KU KARANTA: Karamin minista Kachikwu ya soki NNPC kan karin kudin mai

Yazu haka dai gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali wajen samar da jiragen ruwan yaki ga rundunar ruwan sojojin Najeriya. A karo na biyu katafaren jirgin yakin da Najeriya ta sayo daga kasar China, ya isa kasar Angola kan hanyarsa ta zuwa Najeriya.

Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Komanda Christan Ezekobe, yace rundunar sojojin ruwan Najeriya suna ci gaba da samun manyan jiragen yaki irin na zamani da ake ji da su a wannan karni. Ya kuma ce jirgin farko ya isa Najeriya a bara, wannan kuma gashi yana kan hanya, wanda idan aka kaddamar da su zasu taka rawa sosai wajen samar da tsaro ta cikin ruwa.

Yanzu dai sojojin ruwan Najeriya zasu fara sintiri har zuwa gabar kotun Guinea. A cewar kwararre kan sha’anin tsaro Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa, aikin sojojin ruwa ne su kula duk wani abu dake faruwa ta cikin ruwa, wanda kuma ya hada da matsalar da ake samu a yankin Niger Delta inda ake fasa bututun mai ana kuma satar danyen Mai.

Hakan yasa shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari, yayi aniyar kara musu karfi ta hanyar samarwa rundunar jiragen zamani don samar da tsaro ga jiragen dake sintiri ta kan ruwan kasar.

A wani labarin kan tsaro kuma, Rundunar sojin Najeriya ta ce wani jami'inta ya harbe wata mace 'yar kunar-bakin-wake da ta yi yunkurin tayar da bam a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka ya aikewa manema labarai, ta ce an harbe matar ne a yayin da take yunkurin shiga wani sansanin soji da ke Yamtake a karamar hukumar Gwoza.

A cewarsa, hakan ya faru ne jim kadan bayan soji sun dakile wani hari da 'yan ta'adda suka yi yunkurin kai wa.

Sanarwar ta ce sojojin sun kashe maharan guda hudu, cikinsu har da 'yan kunar-bakin-wake biyu sannan suka kwace bindigogi da alburusai da kuma miyagun kwayoyi daga wajen su.

Sai dai Kukasheka ya kara da cewa soja daya ya rasa ransa a lokacin ba-ta-kashin.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel