Mutane 40 sun mutu a jihar Zamfara

Mutane 40 sun mutu a jihar Zamfara

- Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce kusan mutane arba'in ne aka kashe a cikin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan wata mahakar Zinari.

- Haka ma wasu mutane da dama sun bata yayin da wasu suka tsira da munanan raunukka a cikin harin da aka kai ranar Litinin kan mahakar zinarin wadda ke daura da kauyen Bindim na karamar hukumar Maru.

Mutane 40 sun mutu a jihar Zamfara
Gold mining in Nigeria

Mazauna yankin sun shaida wa majiyar mu cewa harin ya zo bayan da 'yan bindigar wadanda ake zaton 'yan fashin shanu ne suka kwashe makonni suna satar mutane don neman kudin fansa.

'Yawancin wadanda suka mutun lebarori ne masu aikin hakar zinari da kuma wadanda suka zo saye.'' In ji wani mazauni yankin, kodayake kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

A wani labarin kuma Gwamnatin Najeriya na samarwa da rundunar sojojin ruwan kasar manyan jiragen yaki na zamani.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta shirya tsaf don daukar mutanen N-Power 200,000

Yazu haka dai gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali wajen samar da jiragen ruwan yaki ga rundunar ruwan sojojin Najeriya. A karo na biyu katafaren jirgin yakin da Najeriya ta sayo daga kasar China, ya isa kasar Angola kan hanyarsa ta zuwa Najeriya.

Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Komanda Christan Ezekobe, yace rundunar sojojin ruwan Najeriya suna ci gaba da samun manyan jiragen yaki irin na zamani da ake ji da su a wannan karni. Ya kuma ce jirgin farko ya isa Najeriya a bara, wannan kuma gashi yana kan hanya, wanda idan aka kaddamar da su zasu taka rawa sosai wajen samar da tsaro ta cikin ruwa.

Yanzu dai sojojin ruwan Najeriya zasu fara sintiri har zuwa gabar kotun Guinea. A cewar kwararre kan sha’anin tsaro Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa, aikin sojojin ruwa ne su kula duk wani abu dake faruwa ta cikin ruwa, wanda kuma ya hada da matsalar da ake samu a yankin Niger Delta inda ake fasa bututun mai ana kuma satar danyen Mai.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel